Ranar alhamis 22 ga watan Maris majalisar dattawa ta amince da matsayin ta tare wasu sabbin jami'o'i na bankin su uku
Aisha Ahmad yar asalin jihar Niger ta zama mace ta farko mai karancin shekaru da zata yi aikin mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya.
Ranar alhamis 22 ga watan Maris majalisar dattawa ta amince da matsayin ta tare wasu sabbin jami’o’i na bankin su uku.
A cikin watan octoba na 2017 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sunan ta farfajeniyar majalisar tarayya domin amincewa kan nada ta mataimakin gwamnan bankin bayan tsohuwar mai rike da mukamin Serah Alade tayi murabus.
Aisha Ahmad mai shekaru 42 a duniya ta kware a fannin ilimin kudi kana sama da shekarar 20 take aiki a fanin.
Tayi aiki tare da Zenith bank da Diamond, Stanbic IBTC da New york mellon na kasa ingila da Synesix Financial Limited.
Aisha Ahmad Tana da yara biyu tare da mijinta birgediya janar Abdallah Ahmad mai ritaya.
Leave a Reply