Yace kudurin sa wajen kawo gyara a kasar da kuma dora ta matsayin da ya kamace ta ya sanya yake neman sauya shugaba Buhari a zaben 2019
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana dalilin da ya sanya yake a neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019.
Ganawan shi da mabiyan jam’iya PDP na reshin jihar Legas ranar alhamis 22 ga watan Maris, Lamido ya bayyana cewa babban dalilin yunkurin da yake shine don gani ya aiwatar da ayyukan da yan kasa ke bukata kuma ba don dadin mulki ba.
Yace kuddurin sa wajen kawo gyara a kasar da kuma dora ta matsayin da ya kamace ta ya sanya yake neman sauya shugaba Buhari idan Allah ya kai mu zaben 2019.
*INEC ta fitar da jadawalin zaben shugaban kasa da na gwamnoni
Tsohon gwamnan ya soki gwamnatin APC inda yayi ikirari cewa bata biya alkawulan da ta dauka na biyan bukatun yan kasa, don haka ya kamata a canza arkalar shugabancin kasar daga hannun ta.
Yace gwamnatin yanzu ta gaza kan alkawarin da ta dauka yayin da takle yakin neman zaben 2015 wajen tabbatar da tsaro da bunkasa harkar kasuwanci da yaki da cin hanci da rashawa.
Lamido ya bada misalin da tashin hankali da mayakan boko haram ke haifarwa da rikicin makiyaya wajen nuna gazawar gwamnati mai ci.
Tsohon gwamnan yayi kira ga jam’iyar shi PDP data zage damtse wajen tabbatar an cire APC daga karagar shugabancin kasa a zaben 2019.
“Sai Allah ya kama mu idan har muka yi sake APC ta koma mulki bayan zaben 2019” yace.
Ya kuma bukaci yan jamíyar da suyi la’akari da nagarta wajen zabar dan takarar shugaban kasa a taron kasa da zata yi nan gaba.
Leave a Reply